Kotuna musamman don yanke hukunci cikin hanzari a Najeriya
April 22, 2020A wani mataki na ganin an hanzarta aiwatar da hukunci ga masu aikata laifuffuka da ma zama darasi ga na baya a Najeriya, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bukaci sashen shari'a ya kafa kotuna na musamman domin hukunta masu aikata laifuffuka na garkuwa da jama'a da gwagwarmaya da makamai da 'yan fashi a kasar.
Wannan bukata ta kafa kotuna na musamman a Tarayyar ta Najeriyar domin hukunta masu aikata laifuffuka na garkuwa da jama'a da masu gwagwarmaya da makamai musamman masu satan shanu a kasar dai wani mataki ne da aka dade ana cece-cece kuce a kansa.
Barrister Modibbo Bakari kwarren lauya ne mai zaman kansa a Najeriya ya ce batun fa ya wuce na kafa kotuna na musamman, domin "kotunan da ake da su a Najeriya yanzu sun wadatar. Muhimmin abu shi ne 'yan sanda sun gurfanar da masu aikata laifi gaban kotu, da haka ne za a ga ingancin kotu."
Matsala ta rashin aiwatar da hukunci ga masu aikata laifuffuka a Najeriya dai babban al'amari ne a tsarin aiwatar da hukunce-hukunce a Najeriyar musamman ma dai ga mutanen da ake zarginsu da aikata laifuffuka da suka shafi garkuwa da jama'a, matsalar da ke ci gaba da ruruwa tamkar wutar daji a kasar. Shin wane tasiri kafa irin wadannan kotuna za su yi ne a kokari na zama darasi ga na baya da ma rage masu shiga miyagun laifuffuka irin wadannan? Mallam Kabiru Adamu masani ne a fannin harkokin tsaro da na lamura na aikata laifufuka.
"Manufar hukunta mai laifi shi ne horo, sai canja tunaninshi, a koya masa sana'a ta yadda in ya fito wato in mai fitowa ne, zai zama mai amfani ga jama'a. Saboda haka wannan kira da Shugaba Buhari ya yi abu ne mai kyau."
Ga kungiyoyi masu zaman kansu da suke sa ido a kan ayyuka da suka shafi garkuwa da jama'a fashi da makami da ma gwagwarmaya da makamai a yankunan karkara da ta yi naso zuwa ga birane sun dade suna jiran kaiwa ga wannan mataki.
A baya dai shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya gabatar da bukatar kafa kotuna na musamman don yaki da cin hanci da rashawa ba tare da samun nasara ba. Ko a wannan karon zai iya samun haka daga sashen shari'a da ma majalisar dokokin kasar da a baya ta yi karan tsaye a kan wannan bukata?