Najeriya: Majalisa ta amince da kasafin kudin 2018
May 16, 2018Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki shi ne ya jagoranci ‘yan majalisar suka amince da kasafin kudin na wannan shekara ta 2018. Abin da ya kawo karshen dogon jira da ma jinkirin da aka fuskanta na watanni shida bayan gabatar da kasafin kudin da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya yi a ranar 7 ga watan Nuwamban shekarar 2017.
Sanata Ahmed Lawan shugaban masu rinjaye a majalisar ya bayyana irin darasin da ya kamata su koya daga amincewa da kasafin kudin, da ya kai kudi Naira tiriliyan tara da miliyan dubu 100, inda ‘yan majalisar suka yi kari na Naira biliyan 500 daga ainihin adadin da aka gabatar mata tun da farko.
Duk da doki da murna ga kaiwa ga wannan mataki na amincewa da kasafin kudin, ga mafi yawan ‘yan Najeriya na koken rashin gani a kasa, abin da ya sanya Sanata Shehu Sani bayyana cewa dole ne fa a sake lale.
Amma ga ministan kula da wasanni da matasa na Najeriyar Sanata Solomon Dalung ya ce sun dade suna jiran kasafin kudin don haka yanzu za su shiga aiki ne kawai.
A karon farko dai Najeriyar ta kebewa sashen kiwon lafiya kaso mafi tsoka a kasafin kudin, abin da zai iya tasiri ga harkar lafiyar kasar musamman asibitoci da ke cikin mawuyacin hali.