1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dage zaman shari'un zaben gwamnoni a Najeriya

January 13, 2020

Kotun kolin Najeriya ta dage sauraron wasu jerin shari'un zaben gwamnoni da ta shirya a wannan Litinin bayan da wani yamutsi na magoya bayan 'yan takarar ya barke a cikin harabar kotun da ke Abuja.

https://p.dw.com/p/3W9Dt
Gebäude des obersten Gerichtshofs Nigerias in Abuja
Hoto: U.A. Idris


An dai kai har ga kusan bai wa hammata iska ko bayan ihun goyon baya a cikin farfajiyar kotun kolin Tarrayar Najeriya da ta koma fage na sa'insa ta siyasar tarrayar kasar.

Akalla shari'u dai dai guda shida ne dai kotun ta yi niyyar yanke hukunci kafin daga baya hayaniya ta masu siyasar ta tilasta wa alkalan dage ta zuwa gobe Talata. Kama daga Kano zuwa Sokoto da ma Bauchi sannan da Plateau da Imo da Adamawa da kuma Jihar Benue, miliyoyin al'ummar Tarrayar Najeriyar dai na neman sanin gwamnoni na hakika.
Kuma babban fata na cikin zauren kotun kolin inda wasu alkalai guda bakwai a karkashin babban alkalai na kasar ke shirin yanke hukuncin karshe da ma kila kwantar da hankula tsakanin al'umma.

Nigeria Wahlkampf von APC-Partei in Kano
Hoto: Salihi Tanko Yakasai

Kuma dubban magoya baya sun cika daukacin harabar kotun a cikin ihun goyon baya na gwanayensu, abun kuma da ya tilasta wa su kansu alkalan dage shari'au ya zuwa gobe Talata da nufin kai wa ga samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali cikin harabar kotun. Hashim Sulaiman dai ya yi tattaki ya zuwa Abujar domin nuna goyon baya ga Abba Kabir da ke zaman dan takarar Jami'iyyar PDP a Kano, da ya ce fitar da su a zauren kotun bai karya musu gwiwa a cikin shari'ar da suke mata kallon babbar dama ba. Sai dai Barrister Ibrahim Muktar da ke zaman kwamishinan shari'a na Kano daya kuma a cikin masu kallon shari'ar a bangaren gandujiya ba su da hujja ta faduwar gaba a hukuncin.

Nigeria Abba Kabir Yusuf
Hoto: Sanusi Bature

Yamutsin da ya barke a harabar kotun kolin Najeriyar dai a wannan rana ta kai har ga jifan shi kansa tsohon gwamnan Bauchi Mohammad AbdullahI Abubakar da ya shiga kotun yana daga hannun Hurhudu sau biyu amma kuma ya gamu da fushi na masu adawa. Ali M Ali dai na zaman kakakin gwamnan da kuma ya ce suna da babban fata kuma ba su hassala da matakin abokan adawar ba. In har APC na zargin PDP da wuci makadi cikin rawa wajen jifan tsohon gwamna, Ladan salihu kwamishinan labarai na Jihar Bauchi  ya ce babu ruwan 'yan PDP da abun da ya faru da gwamnan.

Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa a tsakanin manyan jam'iyyun da banbancin nasu ke zama kalilan a cikin Tarrayar Najeriyar da batu na siyasar ke kara daukar hankali.