Najeriya: Majalisa ta yi watsi da karin shekarun mulki
November 22, 2024Kudurin wanda Hon Ikenga Ugo Chinyere ya gabatar, yana gama karanta shi aka yi fatali da shi kamar haka.
Kudurin dokar dai ya nemi da a yi wa sassa na 76 da 132 da 136 na kundin tsarin mulkin Najeriyar gyaran fuska domin bada damar mayar da wa'adin mulki na shugaban Najeriya zuwa wa'adi daya na shekaru shida tare da tsarin karba-karba yadda idan yankin kudancinn Najeriya ya yi mulki sai a koma sashin arewacin kasar, duka a kokarin rage kashe kudi da ke tattare da tsarin dimukurdiya.
To sai dai duk da wtasi da kudurin Hon Ikenga Ugo Chinyere ya ce za su sake shiri don tunkarar lamarin.
Kafin kai wa ga wannan mataki dai sun ta zagaya sassan Najeriya inda suka fara samun goyon baya a kan wannan tsari musamman sanin tsadar da ake ganinn tsarin dimukurdiyyar Najeriya na da shi a cikin kasar. Ra'ayoyi dai sun sha bambam a kan wannan batu domin tuni wasu fitattun ‘yan siyasa ciki har da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar suka fara nuna goyon bayansu a kan tsarin. .
Masu rajin kare dimukurdiyya a Najeriyar dai sun dade suna nuna damuwa a kan yadda ake tafiyar da tsarin a cikin kasar wanda baya ga tsada alummar kasar na koke na rashin gani a kasa. Salihu Dantata Mahmoud wanda ke cikin gamaiyyar kungiyoyin farar hula masu rajin kare dimukurdiyya ya ce sun hango alkhairi a cikin matakin da aka dauka.
Yan majalisar 31 da suka gabatar da kudurin na kokarin sake shiri domin tunkarar majalisar tare da neman goyon baya da kamun kafa a kan wannan batu, sai dai wasu na zargin akwai wata kulalliya a cikin lamarin.