1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da hana NYSC

Uwais Abubakar Idris LMJ
June 9, 2021

Majalisar kungiyar matasa masu fafutukar wanzar da zaman lafiya a Najeriya, ta jagoranci wata zanga-zangar lumana a Abuja fadar gwamnatin kasar, domin nuna rashin amincewa da kudurin dokar neman daina yin hidimar kasa.

https://p.dw.com/p/3uf7j
Nigeria Nationalversammlung Abuja
Majalisar dokokin Najeriya, na duba yiwuwar soke shirin yi wa kasa hidimaHoto: AFP/Getty Images/P. Ojisua

Tuni dai majalisar dokokin Najeriyar ta fara aiki kan wannan kudirin doka, abin da ya sanya matasan yin dafifi a gaban majalisar suna rera take na hadin kai tare da daga tutocin Najeriyar, abin da ke nuna bukatar hadin kai ta wannan shiri na yi wa kasa hidima. Dan majalisa Awaji Inombek da ya gabatar da kudurin ga majalisar dai, ya dangata dalilansu a kan rashin tsaro da ya sanya a yanzu ana tura masu yi wa kasa hidimar yankunansu na haihuwa, abin da ya rusa dalilan kafa shirin a 1973. To sai dai Imrana Haruna  da ke cikin wadanda suka jagorancin zanga-zangar ta lumana yace su ba su yarda da wannan uzurin ba.

Nigeria Regionalwahlen 2019
Matasa ma su yi wa kasa hidima, kan yi ayyukan zabe da na kidayaHoto: Reuters/A. Sotunde

Wannan lamari dai ya rarraba kawunan 'yan Najeriyar tsakanin masu goyon bayan soke shirin yi wa kasa hidimar da masu adawa da hakan. Kungiyar Kwadagon Najeriya na cikin masu nuna adawa da wannan ra'ayi. Tuni dai aka yi wa wannan kudurin dokar karatu na daya, inda ake jiran yi masa karatu na biyu kafin kai wa ga sauraron jin ra'ayin jama'a. Masu zanga-zangar dai sun mikawa shugabanin majalisar takardar neman a yi watsi da wannan kudiri. Tun a shekarar 1973 ne dai, aka bullo da shirin yi wa kasa hidimar wato NYSC da ya zama dole a tura duk wanda ya kammala karatun jami'a da na HND a Najeriya zuwa wani sashi na kasar, a bisa dalili na samun hadin kan kasa a tsakanin matasa.