Shugaba Buhari ya rantsar da ministocinsa
August 21, 2019Talla
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a wannan Laraba ya rantsar da membobin majalisar ministocinsa inda ya nada sabon mukamin karamin ministan albarkatun mai a majalisar mai ministoci 43.
Har yanzu dai Shugaba Buharin ne zai ci gaba da rike mukamin ministan mai kamar yadda yake tun a wa'adin mulkinsa na farko, sai dai ya nada Timipre Silva a matsayin ministan kasa na albarkatun mai.
Shi dai Silva da ke zama tsohon gwamnan jihar Bayelsa, ya maye gurbin Emmanuel Kachikwu da ya kasance wakilin Najerya a kungiyar OPEC.
Zainab Ahmed za ta ci gaba da rike mukaminta na ministar kudi.