Najeriya na biyan diyyar asarar EndSars
October 20, 2021Shekara daya ke nan cur da zanga-zangar da matasan suka yi da ake yi wa lakabi da Endsars, wacce ta yi dalilin zargin karkashe mutane da dama a unguwar Lekki da jami'an tsaro suka yi, zargin da har yanzu da ake juyayi na tunawa da abin bakin ciki da ya faru, gwamnatin Najeriya ke musanta kissan masu zanga-zangar.
Ministan yada labaru da al'adun gargajiya na Najeriya Lai Mohammed ya ce har a yau suna kalubalantar a kawo masu shaida ko kuma ‘yan uwan wadanda suke zargin an kashe ‘yan uwansu. Ya bayyana matakan da gwamnati ta dauka da suka hada da alkawarin biyan diyya da aka fara.
Sai dai kungiyar Amnesty International ta bayyana cewa ba ta fara gani a kasa ba a dukannin wadanan abuwa da gwamnatin ke ambaton ta yi, domin jerin alkawuran da aka yi ba a kaiga cikawa ba, a cewar Auwal Musa Rfasanjani, shugaban kungiyar ta Amnesty Interntional a Najeriya.
Tun da farko dai sai da daraktar kungiyar ta Amnesty International, Osai Ojigbo ta fara da batu na bukatar kamata adalci ga wadanda suke zargin an ci zalinsu da ma kisa, domin suna da shaida a hannu da suka gabatar.
Sanin cewa gwamnatin Najeriyar da kungiyoyin kare hakin jama'ar da ma matasan da suka yi zanga-zangar na ci gaba da nuna wa juna ‘yar yatsa.
Ya zuwa yanzu dai jihohi 29 na Najeriya, sun kafa kwamitocin da ke sauraron korafe-korafe na cin zalin da cizgunawa da ma zargin kashe masu zanga-zangar inda 25 daga cikin su suka kammala wannan aiki.
Za a sa ido a ga sauyin da zai biyo baya ta yadda za a koma wancan tsari na dan sanda abokin kowa a Najeriyar ta hanyar kare hakokin jama'a da mutunta juna da mahukuntan ‘yan sandan ke alkawarin dukufa a kansu.