1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar karin kayan aiki ga 'yan sandan Najeriya

February 27, 2020

Rundunar 'yan sandan tarrayar Najeriya ta ce tana bukatar manyan motoci masu sulke 1000 da bindigogi kusan dubu 100 da na'urorin zamani a kan hanyar kai karshen matsalar rashin tsaron tarrayar Najeriya.

https://p.dw.com/p/3YXsI
Symbolbild Nigeria Polizei
Hoto: imago/Xinhua

Wasu  jihohin tarrayar najeriyar dai sun kira komawa zuwa ga 'yan sanda na unguwanni bayan kashe dubban miliyoyin Nairori na cikin tsarin tarrayar, a yayin kuma da wasun ke cewar kato da gora na zaman mafitar kai karshen rikicin.

To sai dai kuma a karon farko rundunar 'yan sandan Najeriyar ta ce akwai jan aiki a kokarin iya tunkarar matsalar rashin tsaron da ke rikida daga sashe ya zuwa sashe na kasar.

Rundunar dai ta ce tana bukatar karin manyan motoci masu sulke kusan dubu daya da kuma bindodin harbi sama da dubu 100 da ma ragowa ta fasaha ta zamani a kan hanyar tunkarar rashin tsaron kasar da ke dada tasiri cikin kasar a halin yanzu.

Hajiya Na'ajatu Mohammed na zaman wakiliya a hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta kasar kuma a tunaninta da sauran tafiya a tsakanin kasar da kaiwa ga tsaro duk da bukatar 'yan sandan da a cewarta ke kamar mafarkin rana.

Nigeria Sicherheitskräfte Kampf gegen Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP/Q. Leboucher

Duk da cewa batun tsaron na cikin manyan alkawuran 'yan mulkin tarrayar Najeriyar zuwa talakawa na kasar, har ya zuwa yanzu dai kasar na da 'yan sandan da ba su wuci dubu 350 ba ga 'yan kasa kusan miliyan 200.

Can a jihar Neja da ke zaman ta kan gaba ga batun rashin tsaron a halin yanzu, gwamnan jihar Abubakar Sani Bello ya ce 'yan sanda 4,000 kawai ke a gare su ga jihar da ke bukatar 'yan sanda kusan dubu 14 abin kuma da ke nuna irin jan aikin da ke gaban mahukuntan.

Tarrayar Najeriyar dai ta ce tana shirin daukar karin 'yan sanda dubu 40 da nufin cike gibin da kila ma rage tasirin sojoji a kokari na kwantar da hankulan al'umma.

Jihar Borno da ke zaman ta kan gaba ga batun rashin tsaron tarrayar Najeriyar da kuma tuni ta koma ga addu'a bayan nuna alamu na gazawa ta 'yan tsaron, kuma tuni sun fara ganin alamun haske a fadar gwamnanta Farfesa Babagana Umara Zullum.

Batun rashin tsaron dai na zaman daya a ciki na tarnaki ga kasar da ke neman zuba jari na waje amma kuma ba ta da karfin kare jarin 'yan jari hujjar na waje.