Kotu ta amince da sake tsara bayanan na'urar BVAS
March 8, 2023Wannan hukunci da kotun daukaka karar ta Najeriya ta yanke ya zama raba gardama a kan wannan batu da ake kiki-kaka a kansa, domin da wannan hukumar zabe ta samu uzuri na sake tsara bayanan da ke cikin na'urar ta Bvas domin su dace da zaben gwamnoni da za'a yi a jihohi 30 na Najeriyar.
Alkalan kotun su uku da suka amince da hukuncin karkashin jagorancin mai sharia Joseph Ikeyegha sun ce ba za'a hanawa hukumar zabe wannan ba saboda zaben.
Dan takarar neman shugabancin Najeriyar Peter Obi dai ya kasance a kotu wajen shari'ar da aka yi ta daga lokacin farawa daga karfe 2 na rana har zuwa 4:30 tare da lauyansa Barrister Anechebe wanda ya wakilci Obin.
Wani batu da kotun ta yi hukunci shi ne na izinin da jamiyyar Labour ta nema na bata izinin dubawa da kwafan takardun zaben.
A wata shari'ar daban kotun daukaka karar ta amince da bukatar zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya duba kayayyakin zaben da aka yi na shugaban Najeriya a wajen hukumar zaben kasar.