Najeriya: Shirin soma bincike a kamfanin NNPC
August 14, 2015A Najeriya sabon shugaban kamfanin man fetir na Ƙasar Emanuel Kachikwu, ya ba da sanarwar shirin gudanar da binciken asusun ajiya na kamfanin na NNPC . Ya bayyana wannan aniya tasa ce a wata Hira da ya yi da manema labarai a birnin Abuja, inda ya ce matakin zai kasance na ba sani ba sabo da zai bincike hatta Ƙananan ma'aikatan kamfanin. Kuma shirin zai shafi shekara ta 2014 da ta 2015 dama kuma illahirin kwangilolin na raba arzikin man fetir da ƙasar ta Cimma da kamfanonin da ke aikin haƙar man fetir a ƙasar ta Najeriya.
A farkon wannan wata na Ogusta ne dai Shugaban ƙasar ta Najeriya Muhamadu Buhari ya kori tsaffin shugabannin kamfanin na NNPC tare da naɗa masa sabon babban darakta da nufin tsarkake kamfanin . Najriya dai wacce ke hako ganga miliyon biyu ta man fetir a ko wane yini na a matsayin ƙasa ta farko wajan arzikin man fetir a Nahiyar Afirka. Kuma shi ne kashi 90 daga cikin dari na hajojin da ƙasar ke sayar wa a ƙasashen ƙetare.