Dakatar da karin hako man fetir
February 22, 2022Talla
Karamin ministan mai a tarayyar Najeriya, Timipre Sylva ya bayyana haka ne inda ya ce babu bukatar kungiyar ta kara adadin yawan man da suke hakokwa duba da ana gab da cimma matsaya tsakanin Iran da kasashen duniya a kan takadamar makamashin nukiliyarta.
A cewar minista Sylva idan har aka cimma matsaya da Iran wacce itama ke zama mamba a kungiyar ta OPEC to za a sami karuwar mai wanda zai janye karancin shi da ake fama a wasu yankunan duniya.
Yanzu haka a sabili da kamfan man da ake gani ganga guda na danyen man na kamawa a kusan dalar Amirka 100, farashin da ba a ga irinshi ba tun a shekarar 2014.