1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Najeriya za ta fara shirin zare tallafin man fetur

Ubale Musa SB/LMJ
January 19, 2023

A takarda dai miliyoyin 'yan kasar na shirin fara dandana zafi na zare tallafin man fetur a cikin tsakiyar shekarar bana. Inda gwamnatin Najeriya ta ce za ta fara shirin zare tallafin man fetur tun daga watan Aprilu.

https://p.dw.com/p/4MS1H
Najeriya I Tashar mai a birnin Abuja
Tashar mai a NajeriyaHoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

 

Shi kansa kasafin kudin kasar na tallafin da ya kai Trilliyan Uku da doriya dai na shirin karewa ne a watan Yunin, abun kuma da ke nufin sabon babi a cikin harkar man tsakanin al'ummar kasar. To sai dai kuma daga duk alamu kasar tana shirin fara zare tallafin tun kafin nan, tare da ministan kudin kasar Zainab Ahmed tana fadin mahukuntan kasar na kallon yiwuwar diga dan bar shirin na zare tallafin tun a cikin watan Aprilun da ke tafe.

Karin Bayani: Sabon fasalin zuba jari a NNPC

Najeriya Tashar mai a birnin Abuja
Najeriya Tashar maiHoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Ya zuwa yanzun dai mahukuntan Najeriyar na fatan kamallagyara na matatar mai ta fatakwal mai ta ce ganga dubu 60,000 a kusan kullum da kuma fara aikin 'yar uwarta da ke Kaduna, ko bayan kaddamar da wata sabuwa ta kamfani na Dangote a karshen watan nan na iya sauya da dama cikin kasar da ke dogaro da tattacen man waje.

Najeriyar dai na fatan samun rarar da ta kai kusan Triliyan Bakwai daga zare tallafin mai tasiri ga makoma ta kasar. To sai dai kuma zare tallafin na iya kai wa ya zuwa sabon rikici cikin kasar da kai yake rabe bisa batun. Duk da kokari na dauka ta hankalin 'yan kasar bisa girma ta asarar dai, masu kodagon kasar sun nisa a adawa da shirin da ke iya kai wa ya zuwa kara matsi na rayuwa cikin kasar.

Fito na fito tsakanin mahukunta da masu kodagon tarrayar Najeriyar ne dai ne ya kai ga tilastawa gwamnatin kasar janye batun na zare tallafin can baya. Kuma a fadar Abubakar Aliyu  da ke zaman kwarrare ga batun tattalin arzikin ana bukatar kallon tsaf cikin batun na tallafi da ke kama da damfarar miliyoyin 'yan kasar a lokaci mai nisa

In ban da birane irin Abuja da kila birnin Legas dai miliyoyin 'yan kasa a  halin yanzu dai na sayen man ne bisa farashin da ya doshi Naira 300 kan kowace litar duk da tallafin da ya kai a kayyade farashin man bisa Naira 185 kowace lita.