1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biliyoyin Naira don aikin gyaran majalisar dokokin Najeriya

Uwais Abubakar Idris MNA
December 17, 2019

Kebe tsabar kudi har Naira biliyan 37 domin gyaran majalisar dokokin Najeriya ya sanya maida martani musamman ganin cewa Najeriya za ta ciwo bashi ne don aiwatar da wani kaso na kasafin kudinta na shekarar 2020.

https://p.dw.com/p/3UxjK
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

A Najeriya kebe tsabar kudi har Naira bilyan 37 domin gyaran majalisar dokokin Najeriya da za a yi wanda aka kasafta a kasafin kudin kasar ya sanya maida martani musamman sanin cewa Najeriya za ta ciwo bashi ne don aiwatar da wani kaso na kasafin kudin na shekara mai zuwa.

Wannan aiki na yi wa daukacin ginin majalisar dokokin Najeriyar da ya hada da majalisar wakilai da ta dattawa da aka kasafta kashewa wannan kudi ya biyo bayan abin da majalisar ta kira tabarbarewar ginin majalisar da ke bukatar a ceto shi daga lalacewa.

Shugaban majalisar Sanata Ahmed Lawan da ya sanar da hakan ya ce shugaban Najeriyar ne Muhammadu Buhari ya yi alkawarin gyaran da amincewa a kan hakan. Sanata Ahmed Baba Kaita ya bayyana dalilinsu na yin hakan da cewa "tun gina zauren majalisar ba a taba yi masa gyara ba, da kamata ya yi gwamnatin da ta gabata ta yi amma ba abin da aka yi."

Babban zauren taro na majalisar dattawan Najeriya
Babban zauren taro na majalisar dattawan NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

To sai dai tuni wannan batu ya sanya maida martani a tsakanin 'yan Najeriya da ke ganin kudin fa sun yi yawa sosai, musamman sanin cewa Najeriya sai ta ciwo bashi kafin ta samu uzurin aiwatar da kasafin kudin shekara mai zuwa. Malam Abubakar Ali masani ne a fannin tattalin arziki a Najeriyar.

"Rashin jin tausayin talakan Najerya ne ya kawo wannan wai a ce za a kashe makudan kudade don yin wannan gyara. Ana ta ciwo bashi kan bashi don a aiwatar da wannan aiki."

Zargi na kambama kudi a duk aiki da ya shafi bada kwangila a Najeriyar na zama daya daga cikin matsalolin da har yanzu ake koke a kansa, duk kuwa da kafa hukuma ta musamman da ya kamata ta duba irin wadannan aiyyuka. Ga Mallam Elharun Muhammad masanin ci gaba da tsare-tsaren kasa ya ce akwai abin dubawa.

"Wannan bayani ya zo da mamaki. Duba da kudade masu yawa sosai da za a kashe. Shin wane irin gyara ne za a yi? Shin ita majalisar na bukatar wannan gyara ne har da za a kashe mata wannan kudi? Ga batun karin albashin ma'aikata har ynzu ana kai ruwa rana kai."

Kasafin kudin Najeriyar dai da daga cikinsa ne za a samar da wadannan kudade tuni aka hango zai samu gibi na kasha 1.52, wanda dama kudaden kiyasi ne ba wai ana da su a hannu ba ne.