Kisan mutane a yaki da ta'addancin Najeriya
December 26, 2024Mazauna yankin da jiragen sojan Najeriya suka kai hari bisa kuskure ne dai suka yi wannan korafi, tare da bayyana bakin ciki a kan yadda sojoji ke gudanar da aikinsu ba tare da an sanar da su ba. To amma kuma cikin wata sanarwa da rundunar sojan Najeriyar mai yaki da 'yan ta'addan Lakurawa mai suna Operation Fansan Yamma ta fitar, ta ce ko shakka babu 'yan ta'addan na Lakurawa na yada zango da ma yin sansani a wannan yanki. Hotunan mutuwar mutane 10 da raunata shida da kuma konewar dabbobi sun fusata 'yan kasa da kungiyoyin kare hakkin dan Adam, ganin cewar wannan ba shi ne karon farko da ake samun sojojin Najeriyar na kuskuren cilla makaman da ke fadawa kan fararen hula maimakon 'yan ta'addan. Masana tsaron kasa sun ce, idan ana ci gaba da samun irin wadannan matsaloli a cikin kasa, akwai matakan da ya kamata ace hukumomi sun dauka. Karamar hukumar Silame dai na daga cikin kananan hukumomi hudu a jihar Sakkwato da 'yan ta'addan Lakurawa ke shawagi a wani daji mai suna Surame, inda sojojin ke kai komo da tankokin yaki da nufin kakkabe su kafin afkuwar wannan iftila'i.