Zanga-zangar #RevolutionNow da martanin gwamnati
August 5, 2019Duk da cewar dai sun yi nasarar kame babban jagoran gwagwarmayar, Omoyele Sowore, jami'an tsaron Tarrayar Najeriyar sun share kusan wunin ranar Litinin suna kokarin murkushe wata zanga zangar da aka wa lakabi da #RevolutionNow da ke neman sauyin da tushenta ke zaman kudanci na kasar.
'Yan juyin dai sun ce dole ne a mai da farashin mai da wutar lantarki zuwa yadda yake kafin komawar dimukuradiyyar kasar a shekarar 1999.
Masu zanga-zangar na kuma neman yanke hukunci na kisa ga barayi na kasar da kuma haramta musu neman mukami na siyasa a nan gaba.
Can kuma a siyasa dai kungiyar mai taken #RevolutionNow ta ce dole ne mulki ya koma hannun talakawa na kasar sannan kuma ya zama wajibi rushe majalisar dattawa ta kasar tare da mai da Tarrayar Najeriyar zuwa tsarin majalisa guda daya.
To sai dai kuma zanga-zangar da jami'an tsaron suka ce na kama da cin amana ta kasa dai ta gamu da fushi na hukumomi a wasu birane na kasar.
Gwamnatin ta Abuja dai ta ce babu batun gyara kayanka cikin rikicin da ke kama da siyasa, sannan kuma ke da burin kai karshen mulkin gwamnatin kasar.
Daga dukkan alamu dai zanga-zangar ta gaza tasirin da ake tunanin samu, musamman ma a sashen arewacin kasar inda ko dai ruwa ya hana fita, ko kuma rashin imani ya kau da hankalin al'umma.
Tuni dai manyan kungiyoyin kwadagon kasar suka nesanta kansu daga zanga-zangar, sannan kuma gwamnatin kasar ta ce tana shirin tuhumar duk wani mai zanga-zangar da laifi na cin amana ta kasa.
Barrister Baba Dala lauya ne mai zaman kansa a Abuja da kuma ya ce duk da cewar kundin tsarin mulki na Najeriya ya ba da 'yancin taro, amma kuma duk wani kokari na sauya tsari na kasar na zaman wuce gona cikin iri.
Tarrayar Najeriyar dai ta yi nisa a cikin rabuwa bisa bambanci na siyasa da ma rigingimu na akidar da ke barazana bisa makoma ta kasar.