Nakiya ta kashe rayuka a Turkiyya
October 15, 2022Talla
Alkaluman mutanen da suka mutu sakamkon fashewar wata nakiya a ma'aikatar sarrafa makamashin kwal a ardin Bartin da ke arewacin kasar Turkiyya ya kai mutum 40 a yanzu.
Bayanai sun ce akwai ma'aikata akalla 110 wadanda ke aiki a lokacin da hadarin ya auku a ranar Juma'a.
Har yanzu nan kan kokarin zakulo wasu mutunen da suka makale a karkashin baraguzan gine-gine, a cewar ministan kula da al'amuran cikin gida a Turkiyyar, Suleyman Soylu. Ana kuma shirye-shiryen jana'izar wadanda suka mutun.
Hukumomi sun ce suna daukar abin a matsayin wani hadari na aiki, amma kuma tuni an kaddamar da bincike domin sanin musabbabinsa.
An kuma baza masu aikin ceto a yankin ciki har da wasu kwararrun aka dauko daga makwabta.