1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nancy Pelosi ta gana da Paparoma Francis

Binta Aliyu Zurmi MAB
October 9, 2021

Paparoma Francis ya gana da kakakin majaliyar dokokin Amirka Nancy Pelosi a daidai lokacin da take shan suka daga limaman katholika na kasarta sakamakon goyon bayan janye dokar hana zubar da ciki ga mata.

https://p.dw.com/p/41Tsx
Nancy Pelosi
Hoto: Getty Images/AFP/J. Watson

Ganawar Shugaban darikar katolika da Pelosi na zuwa ne a daidai lokacin da wata kotun daukaka kara ta tarayya a Amirka, ta yanke hukuncin ba wa jihar Texas damar ci gaba da haramta wa mata yawan zubar da ciki, matakin da ke zuwa kwanaki biyu bayan wata kotu ta dakatar da dokar.

Gwamnatin Biden da Pelosi sun bukaci alkalan babbar kotun kasar da su yi watsi da sabuwar dokar jihar Texas wacce ta hana zubar da ciki daga makonni shida, tana mai cewa ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar. Wata kotun daukaka kara mai ra'ayin mazan jiya ta dawo da haramcin tun a ranar Jumma'a  .

Shugaban Amirka Joe Biden shi ma zai gana da Paparoma Francis a birnin Rome yayin taron kolin kasashe masu karfin taron tattalin arziki na G20 da ke tafe a karshen wannan wata.