An fara isar da kayan agaji Kabul
October 13, 2021A wannan Laraba aka yi nasarar isar da kayayyakin agaji ga iyalan da rikicin kasar Afghanistan ya tagayyara, daruruwan da aka tsugunar a wani sansani na wucin gadi a Kabul babban birnin kasar, sun sami tallafi na abinci da barguna dama kudi, wanda shi ne karon farko da ake isar da agaji a cikin kasar tun bayan janyewar sojojin Amirka da kawayenta daga cikin kasar.
Tallafin bai kai ga dubban 'yan Afghanistan da ke cikin tsanani na bukatar taimako ba inji Babar Baloch na Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.
Kafin Taliban ta kwace mulkin kasar, kusan rabin al'ummar kasar na fama da talauci inda da dama suka dogara da agajin da suke samu daga kasashen waje, sai dai lamarin ya kara lalacewa, tun bayan rikicin da yanzu ya raba mutum fiye da dubu hamsin da gidajensu a yayin da sanyin hunturu mai tsanani da kasar ke fuskanta ke karatowa.