1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Nasarar halaka 'yan ta'adda

December 5, 2024

Shalkwatar Tsaron Najeriya ta fitar da wani sabon rahoto da ke nuna cewa, dakarunta sun kashe 'yan ta'adda sama da 8000 tare da kame wasu a fagen yaki da ta'addanci.

https://p.dw.com/p/4noTu
 Najeriya | Tsaro | Manjo Janar Olufemi Olatubosun Oluyede
Babban hafsan hasoshin Najeriya Manjo Janar Olufemi Olatubosun OluyedeHoto: Ubale Musa/DW

Sanarwar wannan nasara da Shalkwatar Tsaron Najeriyar ta fitar da daraktan yada labarai na rundunar sojojin kasar Manjo Janar Edward Buba ya aikewa manema labarai, ta bayyana cewa akwai kuma wasu 'yan ta'addan sama da dubu 11 da ta kame gami da tseratar da wasu mutane da ake garkuwa da su har 6,376. Manjo Janar Buba ya ce an cimma nasarar halaka 'yan ta'addan ne, yayin jerin samaman da sojoji suka kai a yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya da Arewa maso Yamma da ma Arewa ta Tsakiya da sauran sassan Kasar. Sanarwar ta kara da cewa sojojin da sauaran jami'an tsaro za su yi dukkanin mai yiwuwa, domin ganin sun kawar da duk wata barazanar tsaro da ake fuskanat ba kawai a arewacin Najeriyar ba har ma da sauran sassan kasar. Sai dai yayin da wasu ke yabawa kokarin da jami'an tsaro ke ikirarin yi, wasu na ganin ya kamata su kara kaimi wajen magance sauran matsalolin tsaro da ake fuskanta a sauran sassan kasar.

Tsaro: Gwamnan Katsina ya magantu

Al'ummomin yankunan da ake fama da kalubalen tsaro sun bayyana gamsuwa da wannan rahoto, inda suka ce yana da nasaba da zaman lafiya da yanzu haka ake mora musamman a sassan Arewa maso Gabashin Najeriyar. Sai da yayin da Shalkwatar Tsaron ke neman hadin kan al'umma domin kara samun wasu nasarorin, Malam Hassan Abdullahi wani masanin tsaro a Najeriya na ganin sai fa dole al'umma sun bayar da tasu gudumawa in har ana son dorewar wannan nasara. To amma Malam Umar Kirawa wani mai fashin baki kan harkokin tsaro, shawartar sojoji da sauran jami'an tsaro ya yi, kan kar su yi sake da wannan nasarar da suka samu saboda har yanzu da sauran aiki a gabansu. Sau da yawa dai Shalkwatar Tsaron na fitar da irin wannan rahoto da ke nuna samun nasara, amma kuma har yanzu akwai kalubalen tsaro da ake fuskanta a sassan kasar. Ko da a 'yan kwanakin nan ma, wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda da ake kira Lakurawa ta bulla tare da haifar da karin barazanar tsaro a kasar.