Ana cigaba da laluben hanyoyin sulhunta rikicin Afghnistan
September 3, 2019Talla
Tuni shugaba Donald Trump na Amirka ya sanar da shirin janye sojoji da yawansu ya kai dubu 8,600 daga kasar idan aka cimma daidaito a sulhun, an dai kwashe fiye da shekara guda tsakanin Amirka da Taliban ana laluben hanyoyin magance rashin jituwar da ke haifar da asarar rayuka da dukiyoyin gwamnati a Afghanistan.
Sakataren kungiyar tsaron ta NATO Jens Stoltenberg ya gana da shugabar hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Turai Ursula von der Leyen a birnin Brussels game da batutuwan da suka shafi alakar kasashen ketare.