1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarain tabbatar da adalci a duniya

December 5, 2018

Amirka ta ce tana aiki tukuru wajen tabbatar da adalci a duniya lamarin da yanzu ke fuskantar tirjiya sakamakon barazana daga wasu kasashe.

https://p.dw.com/p/39X02
NATO Gipel in Brüssel
Hoto: Reuters/Y. Herman

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya bayyana cewar gwamanatin Shugaban Donald Trump tana aiki tukuru wajen tabbatar da adalci a duniya lamarin da yanzu yake fuskantar tirjiya sakamakon barazana daga wasu kasashe. Ya bayyana hakan yayin da yake jawabin a Brussels a taron ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar tsaro ta NATO.

Yayin wani jawabin a birnin na Brussels, Mike Pompeo ya tabo batutuwa da dama, kana ya ce dole ne Amirka ta mike don ganin ta yaki cin zarafi da kasashen Rasha da China da kuma Iran ke yi a duniya. Wannan ne yasa shuganan Amirka Donald Trump himmatuwa don ganin ya dawo da martabar shugabanci da kasar ke da shi a duniya, kuma yayi kira ga kawayen Amirka da su taimaka wa yunkurin gwamnatin Shugaba Trump wajen tabbatar da adalci a hukumomi kamar su hukumar kula da kasuwanci ta duniya, da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da kuma asusun ba da lamuni na duniya don ganin suna biyan bukatun da ya kamata. A cewarsa rashin kulawar da suke ce tasa wasu ke cimma muguwar aniyarsu.

Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar NATO a taron da suka yi a Brussels
Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar NATO a taron da suka yi a BrusselsHoto: Reuters/Y. Herman

Wannan maganar da Pompeo ya yi a gaban jami'an diflomasiyyar kungiyar NATO, na zama kamar wani hannunka mai sanda ga kasashen Rasha da Iran da kuma Sin wato China. Ya kuma kara da cewa abin da ke faruwa yanzu gazawar da suke nunawa ce ta haifar.

Wannan jawabin nasa ya zo daidai lokacin da kungiyar NATO ke taro don tattauna batun tsamin dangantaka da aka samu tsakanin Rasha da kasar Ukraine biyo bayan takardama da aka samu da sojojin ruwan Ukraine.

Kazalika janyewar da kasar Amirka ta yi daga wata yarjejeniyar nukiliya da aka kulla a shekarar 1987 a matsayin martani ga kasar Rasha saboda saba wasu ka'idoji, na zama wata barazanar tsaro ga daukacin  kasashen nahiyar Turai.

Duk da cewa duniya ta zargi Amirka na ficewa daga yarjejeniyar nukiliya da Iran da kuma yadda kasashen duniya ke kallon Amirka a matsayin tana kare bukatun kanta kawai.