1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta yi tir da harin Rasha kan Ukraine

Abdullahi Tanko Bala
February 24, 2022

Kungiyar tsaro ta NATO ta sanya dakarunta cikin shirin ko ta kwana bayan harin da Rasha ta kai cikin kasar Ukraine

https://p.dw.com/p/47Yo3
NATO Generalsekretär Jens Stoltenberg
Hoto: John Thys/AFP/Getty Images

Shugabannin kasashen duniya sun baiyana martani ga mamayar da Rasha ta yi wa kasar Ukraine ta sama ta kasa da kuma ta ruwa inda suka ci alwashin sanya mata tsauraran takunkumi.

Shugabannin sun kuma yi alkawarin kare sojojin Ukraine ba tare da yakin ya ta'azzara a fadin nahiyar Turai ba.

Tuni kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta sanya dakarunta a gabashin Turai cikin shirin ko ta kwana.

Kungiyar ta kuma kira taron koli na shugabannin kasashe mambobin NATO bayan da shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi kashedi game da tsoma bakin wasu kasashe cikin rikicin yana mai cewa muddun suka kuskura suka shiga zai haifar da mummunan sakamako da ba a taba gani ba a tsawon tarihi.