Navalny ya yaba jinyar da ake yi masa
September 19, 2020Talla
Mr. Navalny mai shekaru 44, ya jinjina wa kasar Jamus musamman da kasancewa da hazikan likitoci, a sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram. Ya nuna jin dadin yadda sannu a hankali yake murmurewa.
A kwanakin da suka gabata dai jagoran adawar Rashan, ba ya iya gane mutane ko iya magana.
Sai dai ya ce murmurewar tasa za ta dauki lokaci kafin ya iya samun lafiyarsa yadda yake bukata.
Sakon na Alexie Navalny dai ya samu karbuwa daga dubban masu bin shafin nasa, cikin dan kankanin lokaci da wallafa shi.