Navi Pillay ta fara ziyara a Sudan ta Kudu
April 28, 2014Talla
Ms. Pillay da mazon Majalisar Dinkin Duniya na musamman mai kare kisan kare dangi Adama Dieng za su tattauna da Shugaba Salva Kiir da wasu manya 'yan siyasar kasar, baya ga ziyarar gani da ido da za su kai wuraren da aka yi kashe-kashen.
A makon da ya gabata dai kwamitin sulhu ma Majalisar Dinkin Duniya ya yi barazanar sanya takunkumi ga wadandan ke da hannu kan rikicin Sudan ta Kudun musamman ma dai dakarun gwamnatin Shugaba Kiir da 'yan tawaye da ke goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Pinado Abdu-Waba