1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sababbin matakan yaki da Boko Haram

Gazali Abdou Tasawa
November 29, 2018

Shugabannin kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru sun yi shelar neman agaji daga kasashen duniya domin fuskantar sabbin hare-haren da kungiyar Boko Haram ke zafafawa a bayan nan a yankin Tafkin Chadi. 

https://p.dw.com/p/39AOi
Nigeria Tschadsee Konferenz
Hoto: State House, Abuja

Shugabannin kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da kuma Firaministan kasar Kamaru sun yi kira ga kasashen duniya da su kawo wa kasashensu dauki, a yakin da suke da kungiyar Boko Haram wacce ke zafafa hare-harenta a baya-bayan nan a yankin na Tafkin Chadi. Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da Mahamadou Issoufou na Nijar da Idriss Deby Itno na Chadi da kuma Firaministan kasar Kamaru Philemon Yang sun yi wannan kira ne a karshen wani taron da suka gudanar a wannan Alhamis a birnin Ndjamena na kasar ta Chadi. A ganawar da shugabannin suka yi a asirce, sun bayyana damuwarsu dangane da yadda kungiyar ta Boko Haram ke kara karfi. 

Shugabannin kasashe yankin Tafkin Chadin sun kuma tattauna da shugabannin rundunar hadin gwiwar kasahen nasu da ke samun tallafin kasashen Turai ta FMM wato Force Multinationale Mixte a yakin da suke da kungiyar ta Boko Haram a yankin na Tafkin Chadi, inda suka dauki alkawarin yawaita irin wannan haduwa domin tattaunawa lokacin zuwa lokaci kan matakan da suka dace su dauka domin karya lagon kungiyar.