Neman hanyar dakile rikici a mashigin ruwan Koriya
August 12, 2017Talla
Shugaba Xi Jinping na China ya bukaci shugaba Donald Trump na Amirka ya sassauta bakaken kalamai kan mahukuntan kasar Koriya ta Arewa, domin neman hanyoyin sassanta bangarorin biyu masu facaccakar juna. Shugaba Xi ya bukaci haka lokacin da shugaban na Amirka ya kirashi ta wayar tarho, domin neman hanyoyin dakile shirin nukiliya na Koriya ta Arewa lamarin da ya harzika Amirka, musamman ganin yadda shugaba Kim Jong-Un na Koriya ta Arewa yake bazarana kan muradun Amirka da kawayenta. Shugaban na Amirka ya kira gwamnan tsibirin Guam Eddie Calvo da ke karkashin ikon Amirka, domin tabbatar masa da cewar Amirka za ta kare tsibirin daga duk barazana daga Koriya ta Arewa.