Neman kawo karshen rikici
December 28, 2013Tawagar farko ta dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ta isa kasar Sudan ta Kudu, kwanaki uku bayan kudirin Kwamitin Sulhu na majalisar da ya amince da karfafa aikin dakarun domin kare fararen hula da suka tsere daga rikicin dake faruwa.
Tawagar ta kunshi 'yan sanda 72 daga kasar Bangladesh, kuma kimanin dakaru dubu biyar da dari biyar da 'yan sanda 440 za a tura.
A hannu guda kuma shugabannin kasashen gabashin Afirka da suka gudanar da taro na musamman sun ce bisa manufa gwamnatin kasar ta Sudan ta Kudu ta amince da tsagaita wuta nan take. Taron ya nemi Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya gana da tsohon mataimakin shugaban Riek Machar.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, rikicin da ya goce ya kai ga mutuwar fiye da mutane dubu daya, sannan akwai wasu fiye da dubu 100 da suke samun mafaka a sansanobnin majalisar da ke cikin kasar ta Sudan ta Kudu.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh