1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman mafita ga rikicin Senegal

February 23, 2012

Obasanjo dake shiga tsakani a rikicin siyasar Senegal ya gana da gaggan 'yan adawa

https://p.dw.com/p/147xR
Re-elected President Olusegun Obasanjo smiles as he leaves a ceremony where he was presented with a certificate of return by the Independent National Electoral Commission at the INEC headquarters in the Nigerian capital Abuja Wednesday, April 23, 2003. (AP Photo/Ben Curtis)
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun ObasanjoHoto: AP

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, wanda ke ƙasar Senegal domin sanya ido akan zaɓukan ƙasar da za su gudana a ƙarshen mako, waɗanda kuma ake taƙaddama akan su, ya gana da manyan 'yan takarar adawa a wannan Larabar a ƙoƙarin da yake yi na shawo kan fito-na-fiton siyasar dake ƙara zafafa a ƙasar ta Senegal. Sai dai kuma ba'a kai ga samun bayani game da yadda tattaunawar ta gudana ba.

Ana ta gudanar da jerin zanga-zanga ne musamman a Dakar, babban birnin ƙasar tun cikin watan daya gabata, bayan da wata kotu ta lamuncewa shugaban ƙasar Abdoulaye Wade tsayawa takara a wa'adi na ukku, duk kuwa da cewar tsarin mulkin ƙasar ya tanadi wa'adi biyu ne kawai ga shugaban ƙasa.

Shugaba Wade mai shekaru 85 a duniya, ya ƙafa hujjar cewar dokar ba ta hau kansa ba tunda kuwa gyaran tsarin mulkin ƙasar ya wakana ne bayan zaɓan sa.

Ƙungiyar tarayyar Turai ta buƙaci ɗaukacin sassan da abin ya shafa da su kawo ƙarshen tashe - tashen hankulan ƙasar wanda ya janyo mutuwar aƙalla mutane shidda, a yayin da wasu da dama kuma suka sami rauni.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu