1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman shawo kan matsalar Sudan ta Kudu

October 20, 2014

Ana tattaunawa kan kawo karshen rikicin kasar Sudan ta Kudu

https://p.dw.com/p/1DYuM
Hoto: Ashraf Shalzy/AFP/Getty Images

A wannan Litinin bangarorin da ke rikici da juna na kasar Sudan ta Kudu sun gana a birnin Arusha na kasar Tanzaniya.

Kasar ta fada rikici tun watan Disamba lokacin da aka samu sabani tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar. Shugaban kasar ta Tanzaniya Jakaya Kikwete ya gayyaci bangarorin wajen ganawa a birnin Arusha, domin samun hanyoyin warware rikicin kasar ta Sudan ta Kudu.

Yunkurin da aka yi a baya na tattaunawar birnin Addis Ababa na kasar Habasha ya ci tura, amma ana sa ran wannan karon bangarorin za su kai ga wata yarjejeniyar da za ta kawo zaman lafiya wa kasar ta Sudan ta Kudu.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba