Tankiyar samun nasara a zaben 'yan majalisun Isra'ila
April 10, 2019Talla
Rahotannin sun ce bayan kammala kidayar kashi biyu bisa uku na kuri'un, jam'iyyar Likud ta Netanyahu ita ce ke kan gaba a gaban jam'iyyar masu matsagaicin ra'ayi da ake kira Fari da Shudi ta tsohon shugaban soja kasar Benny Gantz. Sai dai a halin da ake ciki a wani taron manema labarai da ya kira abokin adawar na Netanyahu, Benny Gantz shi ma ya yi ikirarin samun nasara.