Netanyahu ya yi ikirarin nasara
March 3, 2020Talla
Firaminista Benjamin Netanyahu ya yi ikirarin samun nasara a zaben da aka yi a ranar Litinin ne daidai lokacin kuma da ake cewa yana da sauran kalubale a gabansa, saboda hasashe na cewa da wuya ne kawancen jam'iyyu masu matsanancin ra'ayi da yake jagoranta, ya iya samun kujeru 61 da ke iya samar da cikakken rinjayen kafa gwamnati.
Baki dayan su dai jimilla, suna da kujeru 59 ne daga abin da aka hasaso ta kafar watsa labaran cikin gida da jijjifin safiyar Talata.
Da fari dai bayanai sun nuna yiwuwar kawancen ya iya samun akalla kujeru 60 ne cikin 120 da ake da su a majalisar.
Yayin da shi kuwa abokin hamayyar Mr. Netanyahu, wato Benny Gantz da gamayyar jam'iyyun da ke bangarensa, hasashen ke cewa ba za su wuce samun kujeru 54 ba.