Isra'ila ta yi watsi da kudirin MDD
December 24, 2016Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma'a ya bukaci Isra'ila ta tsaida duk wasu gine-gine da take yi a yankin Falasdinawa, abin da ke zuwa bayan da Amirka ta zama 'yar ba ruwanta cikin mambobi 15 na kwamitin, sabanin yin karfa-karfa da ta saba dan kare muradu na babbar kawarta a yankin Gabas ta Tsakiya. Wannan dai ya sanya cimma matsaya guda da ke zama ta farko a majalisar tun a shekarar 1979 dan yin adawa da tsarin mamayar ta Isra'ila a yankin na Falasdinu.
Tuni dai Firaminista Benjamin Netanyahu ya fito da yin Alla-wadai, da ma yin watsi da matsayar da Kwamitin Sulhun na MDD ya cimma, inda ya ce ba za su mutunta abin da tanadin ya kunsa ba, zai kuma duba yadda sabon Shugaban Amirka Donald Trump zai goyi bayansu a nan gaba. Daga bangaren na Falasdinawa jakadansu a MDD Riyad Mansour, ya ce abin da ya rage yanzu shi ne bibiya kada Isra'ila ta ki mutunta bukatar da aka gabatar mata.