1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Isra'ila zai gurfana a gaban kotu

Abdoulaye Mamane Amadou
November 21, 2019

Kotu a Isra'ila za ta kaddamar da binciken Firaminista Benjamin Netanyahu bisa zargin da ake masa na aikata cin hanci da rashawa da ci da ceto da ha'inci a cikin mulkinsa.

https://p.dw.com/p/3TUiM
Israel | Benjamin Netanjahu
Hoto: AFP/G. Tibbon

Kotu na zargin firaminista Netanyahu ne da aikata laifukan cin hanci da rashawa da almundahana, ciki har da batun nan da ya shafi kamfanin Bezeq wanda ya fi daukar hankali da kuma ke a matsayin irinsa na farko a tsawon tarihin Benjamin Netanyahu wanda ya shafe tsawon shekaru 13 yana tafiyar da harkokin mulki.

Wannan matakin na kotun Isra'ila na zuwa ne a yayin da ake 'yan sa'o'i kalilan bayan da shugaban kasar ta Isra'ila ya bayyana cewa matakin nada firaminista a yanzu ya dogarane kan 'yan majalisun dokokin kasar maimakon hannun mutun guda kawai, a wani yunkuri na warware takkadamar siyasar da dauki dimi a kasar.