Isra'ila: Shirin kafa gwamnatin hadin gwiwa
April 15, 2020Talla
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na da 'yan sa'oi kafin cikan wa'adin kafa gwamnatin hadaka wanda akasin hakan ka iya jefa kasar cikin sabon rudanin siyasa. Samar da gwamnatin hadin gwiwar zai kawo karshen rikita-rikitan siyasa da kasar ta fada tun Disambar 2018.
Mista Netanyahu ya kasa kafa gwamnati ne bayan rashin nasara na isassun kuri'un da za su ba shi zarafin kafa gwamnati ba tare da hada kai da wasu jam'iyyun siyasa ba. Benny Gantz kuwa na jagorancin wata hadakar jam'iyyu ne masu sassaucin ra'ayi, wannan dai dama ce a gareshi ya hada gwamnatin hadin gwiwar a sakamakon gazawar Firaiminista Netanyahu.