Nicaragua ta shigar da karar Jamus a kotun ICJ
March 2, 2024Talla
Gwamnatin Nicaragua ta ce Jamus ta bai wa Isra'ila tallafin yaki yayin da dakatar da bayar da gaji ga hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu na Majalisar Dinkin Duniya, domin hakan ne ta zargi gwamnatin Berlin da taimakawa Isra'ila wajen aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa a Gaza.
Kasar ta kuma zargi Jamus da rashin sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na dokar hana kisan kare dangi na kasa da kasa.
Kawo yanzu dai Jamus ba ta mayar da martani kan karar da aka shigar kanta ba a gaban kotun ICJ. Isra'ila dai ta dade ta musanta zargin da ake mata na aikata kisan kare dangi da ma take hakkin bil Adama a Zirin.