Nigeria: Mata masu aikin tsaro
Shiga fagen aikin maza: Kamfanin tsaro mai suna Dragon Squad yana daukar mata manya karfafa ne kawai wanda ke zama kalubale na tasirin karfi sannan kuma ga kyau.
Hanzarta shirin kawar da tsangwama
Yan kamfanin tsaro na Dragon Squad na horo a birnin Uyo a kudancin Najeriya. Dragon Squad na daukar mata kebabbu masu girman jiki da diri tare da samar musu yanayin tsaro mai inganci.
Tsaro da karfin zuciya
Emen Thomas, wacce ta samar da kamfanin Dragon Squad Limited, na shirin tura tawagarta wurin aiki a lokacin kuruciyarta ta sha tsangwama daga siraran mata yan ajinsu, ta sami tsunuwa a inda jikinta zai yi amfani. A 2018 Thomas ta kafa kamfanin na tsaro wanda ke yi wa mata kadai aiki.
Alamar karfi da kariya
Ma'aikatan Dragon Squad na lika bajen kamfanin a jikin hannun rigarsu. Wadda ta kafa kamfanin ta baiyana hallitar da jikin bajen a matsayin alamar karfi da kariya.
Cikakken tsaro na bankwana
Hikimar ta samu karbuwa: Mai'aikatan Dragon Squad sun yi aiki a wuraren taruka kusan 2000. Ko dai liyafa ko gidan rawa ko tarukan siyasa ko kuma Jana'iza. Ma'aikatan 43 sun tabbatar da taruka a wurare da dama.
Sarakunan gargajiya na cikin ma'abota dakarun tsaro mata
Matan na kamfanin tsaro ba ma kawai suna ba da tsaro wajen taruka ba ne kadai har ma da ba da kariya ga daidaikun mutane masu bukata. A nan Ester Brown da Ukeme Tom suna kare sabon sarki Obon Ibanga Ikpe a lokacin bikin nadinsa a Uyo.
Binciken jiki da sanin ya kamata
A waje, wasu ma'aikatan Dragon Squad su biyu sun tsayar da wani mutum da ke neman shiga wurin manyan baki. Thomas mai kamfanin tsaron ta yi imani mata sun fi iya aikin dogarai sukan warware matsala cikin sauki ta hanyar sauraron bangarori biyu da ke takaddama wanda yawancin maza ba su da hakurin jure haka.
Yaki da tsangwama
Peace Vigorous, 'Yar shekaru 23 da haihuwa kuma mafi karancin shekaru a cikin tawagar na gyara gashin kanta kafin halartar wani aiki a coci. Vigorous ta ce yawanci mutane na tunanin ganin mace ta zauna a dakin girki ko kuma aikin kwalliya. Aikinsu na tsaro wata dama ce ta nuna ci gaban da mata suka samu a fannoni da dama na rayuwa.
"Ka san kanka!"
Aikinta a matsayin mai gadi ya yi tasiri a kan rayuwar Thomas. Kamar takwarorinta da dama ka kasance mai kunya da kuma saboda kibarta. Aikin ya kara mata kwarin gwiwa a cewar matashiyar mai shekaru 37 da ta je dauko danta daga makaranta. Sakon ta shi ne kalli taro kuma ka san kanka.
Atisaye da barkonon tsohuwa
Thomas na jagorantar atisaye a gefen wani wurin wanka, mun kudurce a zuciyarmu za a iya tsokanar mu a wurin aiki. A saboda haka dogaran ba su tsaya ga karfinsu kawai ba suna tafiya da barkonon tsohuwa idan an kira su wurin aiki.
Tsaro ga mata don mata
Wannan mai kwalliyar ba ta damuwa: Jami'an Dragon Squad sun bada cikakken tsaro a wannan wasa da ta ke gudanarwa. Cin zarafin mata na karuwa a Najeriya. Kasar ta yammacin Afirka ta yi kaurin suna a duniya wajen cin zarafin mata. Mai kamfanin na Dragon Squad ta ce aikinta ya karfafa mata gwiwar fafutukar kare hakkin 'yan mata da magidantan mata