Nijar: Ana cigaba da tsokaci kan yunkurin juyin mulki
December 18, 2015Kungiyoyin fararen hula na Nijar dai na daga cikin wanda ke kan gaba wajen tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu inda da damarsu ke cewar yunkurin abin Allah wadai ne. Habila Rabi'u da ke jagorantar wata kungiya da ke kare hakkin matasa ya ce ''wannan lamari kokari na maida hannun agogo baya kuma ya kamata 'yan Nijar su tashi tsaye wajen kare kasar''.
Shi kuwa Masa'udu Ibrahim da ke yin fashin baki kan lamuran yau da kullum a Nijar din ya ce wannan rudani da aka shiga bai zo masa da mamaki ba duba da yadda fagen siyasar kasar a halin yanzu ya ke dumama gabannin zaben shugaban kasar da za a yi a wata mai Fabrairu da ke tafe.
To yayin da wannan batu ke cigaba da dauakr hankali a Jamhuriyar ta Nijar, shi kuwa shugaban jaam'iyyar nan ta MBDN Kokari wadda ba ta cikin jerin jam'iyyun da ke kawance da masu mulki ya ce su abinda suke son ganin an yi shi ne a yi cikakken bayani game da su wanda ake ce sun yi yunkurin juyin mulkin musamman ma sunayensu maimakon a ce ana rara-gefe.
A jawabinsa da ya yi ranar Alhamis din da ta gabata dai, shugaba Mouhamadou Issoufou ya tabbatar da wannan yunkurin na juyin mulki kuma ma ya nuna 'yar yatsa ga jam'iyyun da ke hamayya da shi kan lamari ko da dai 'yan adawar sun musanta wannan zargi nasa har ma suka kira taron manema labarai don fayyace matsayinsu.