Sojin Nijar 12 sun mutu a cikin wani harin Boko Haram
October 30, 2019Talla
Kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA ya ruwaito gwamnan Jihar ta Diffa Malam Issa Lamine kasar ta Nijar na cewa maharan sun kai farmakin ne tun da sanhin safiyar wannan Laraba a kauyen na Blabrime kilomita 45 daga gabashin birnin N'Guigmi inda suka yi nasarar karbe kayayyakin yaki dama.
Sai dai ya kara da cewa sojojin gwamnatin sun shiga farautar maharan daga baya har a cikin Tabkin Chadi inda suka yi nasarar kashe mayakan na boko Haram da dama kana suka karbo kotocin yaki biyu da tarin makamai.