1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar shafukan sada zumunta a Nijar

Gazali Abdou Tasawa LMJ
June 22, 2022

Cibiyar 'yan jaridu ta Jamhuriyar Nijar wato "Maison de la Presse" da wasu 'yan fafutuka da bloggers masu wallafe-wallafe a shafukan sada zumunta, na yin martani kan sabuwar dokar tsarin amfani da shafukan sada zumunta.

https://p.dw.com/p/4D5S9
Facebook da Instagram
Gwamnatoci da dama a Afirka, na kafa dokokin amfani da shafukan sada zumuntaHoto: DAVID H. CALZADA/Zoonar/picture alliance

Majalisar dokokin Jamhuriyar ta Nijar ce dai, ta amince da wannan doka da ta tanadi hukuncin zaman kaso da kuma tara a kan wasu laifukan da kuma dauke wa wasu laifukan zaman kaso. Daga cikin laifukan da sabuwar dokar ta janye hukuncin zaman gidan kaso a kansu, akwai samun mutum da laifin cin zarafi ko zagin wani mutum ta hanyar amfani da shafukan sada zumunta na zamani da tsohuwar dokar ta tanada. Sai dai kuma sabuwar dokar ta yaki da aikata laifuka a shafukan sada zumunta, ta tanadi tara ta zunzurutun kudi da ya kama daga miliyan biyar zuwa miliyan 10 na CFA ga duk mutumin da kotu ta samu da laifin yi wa wani kage ko kazafi ko kuma zaginsa a shafukan sada zumunta a maimakon miliyan biyu zuwa 10 a tsohuwar doka. A wata hira da ya yi da manema labarai sakataren yada labarai na babbar cibiyar 'yan jaridu ta kasa Souleiman Oumarou Brah ya bayyana farin cikinsa da sabuwar dokar, sai dai ya ce suna jira su gani a kasa.

Nijar I Yamai | Majalisar Dokoki
Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta amince da sabuwar dokar kafafen sada zumuntaHoto: Gazali A. Tassawa/DW

Shi ma dai Malam Moudi Moussa dan jarida dan fafutuka kuma blogger a Jamhuriyar ta Nijar cewa ya yi duk da ci-gaban da aka samu, batun tara babbar barazana ce ga makomar fafutuka a kasar ta Nijar. Shi ma wani fitattcen mai wallafe-wallafe a kafafen sada zumunta na zamanin a Jamuhriyar ta Nijar Mamoudou Djibo cewa ya yi, akwai bukatar ci gaba da gwagwarmaya domin ganin gwamnati ta saki ragamar 'yancin walwala a kasar. Sabuwar dokar shafukan sada zumuntan dai, ta kuma tanadi zaman kaso na shekara daya zuwa biyar da kuma tara ta miliyan biyar zuwa 10 na CFA, ga duk mutuman da shari'a ta samu da laifin wallafa wani sako na rubuce ko na murya ko hoto ko wani zane ko kuma bidiyo masu nasaba da kabilanci ko bangaranci ko banbancin launin fata ko na addini ko kuma na kyamar baki da ka iya haddasa tashin hankali a tsakanin al'umma.