1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Inganta rayuwar mata da yara a Nijar

July 9, 2018

Mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed, ta yi rangadi a Maradi don duba ayyukan ci gaban mata da yara.

https://p.dw.com/p/316FV
Amina Mohammed, stellvertretende Generalsekretärin der Vereinten Nationen
Hoto: Reuters/M. Segar

Daga cikin matan da suka dafa wa Amina Mohammed baya cikin wannan ziyara akwai Margot Wallstrom ministar harkokin waje ta kasar Sweden, da wakiliyar kungiyar hadin kan Afirka Fatoumata Bintou, da shugabar kungiyar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin mata ONU FEMME, da Mme Zeinabou El-Back ministar bunkasa rayuwar mata ta Nijar da mataimakiyar shugaban kasar Afirka ta Kudu da dai sauran mata masu rike da mukamai daban- daban masu aiki tare da Amina Mohamed kan bututuwa masu alaka da rayuwar mata da yara a duniya.

Gurin wannan rangadin shi ne ganawa kai tsaye da matan karkara a jihar Maradi, inda kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya ke ayyukansu na agaji ko tallafi dan jin halin da rayuwarsu take ciki, ci gaba ko koma bayar da aka samu.

Bayan haka sun gani da ido muhimman ayyukan da kungiyoyin MDD suka yi na sauyin da hakan ya kawo wa al'umma. Bayan haka a karshe sun tattara koke-koken matan da yara su kai ga shugabanninsu don samo mafita.

Cibiyoyin inganta rayuwar mata da yara

Inganta rayuwar matan karkara na daga cikin burin da duniya ta sa gaba
Inganta rayuwar matan karkara na daga cikin burin da duniya ta sa gabaHoto: Mahamadou Manirou

Tawagar ta mataimakiyar sakataren MDD, Amina Mohammed ta garzaya kai tsaye a garin Bamo Jari Alpta daya daga cikin garuruwan da suka ci moriyar tallafin kungiyoyin MDD, inda ta gana da matan garin kuma ta gane wa idonta ayyukan alheri da dama da kungiyoyin suka gabatar a cikin garin da kewaye, kamar cibiyar waye kai da horar da mata ayyukan hannu, yaki da jahilci, waye kai kan auren gaugawa, yankan dan gurya, sa diya mata karatu, da sauransu.

Mai gari na Bamo dan Jari ya ce shi kam yana daga cikin na sahun gaba wurin ba da goyon baya ga wadannan ayyuka.

Uma Inusa wata budurwa ce da taci moriyar wannan cibiya ta bayyana wa tawagar yadda ta samu kanta a ciki.

Bayan Garin Bamo tawagar ta issa a garin Danja, inda can ma suka jagoranci taro na mata da 'yan mata na garin don jin ci gaban da suka samu da kuma matsalolin da suke fuskanta. An baje musu koli na ayyuka kala-kala da matan garin suka yi da dogaro da kansu. Amina Mohammed ta ce sun ji dadi kuma sun gamsu da wannan rangadi.

Wannan rangadi dai ba karamar sa'a ce ba ga al'ummar jihar Maradi a cewar mai girma gwamnan jihar Maradi Zakari Umaru Garuruwa, wanda ya kara da cewa mutane da dama suke cin moriyar wannan tsari kuma nan gaba kadan za a fadada tsarin a cikin sauran garuruwa.