Nijar: Jirgin ruwa ya kife da mutane
July 11, 2019Talla
Hadarin dai ya faru ne lokacin da ake kokarin hayewa da fasinjojin da ke cikin jirgin. Tuni dai bayanai suka fara fitowa fili game da dalilin kifewar jirgin ruwan inda hukumomi suka ce yi wa jirgin lodin da ya wuce kima ne ya sanya kifewarsa.
Wannan ne ma ya sanya hukumomi a kasar ta bakin gwamnan jihar ta Maradi Zakari Umaru yin kira ga al'ummar yankin kan su guji yin dukannin wani abu da ka iya jawo faruwar irin wannan lamari nan gaba.