1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Matsalar tsige magadan gari

October 21, 2019

Birnin Maradin Jamhuriyar Nijar ya yi kaurin suna wajen fama da tsigewar magadan gari inda ko a makon jiya gwamnatin ta bayar da sanarwar tsige babban magajin garin da'irar birnin bisa zarginsa da aikata laifi.

https://p.dw.com/p/3RfRC
Niger Treffen der afrikanischen Union in Niamey - Mahamadou Issoufou
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou IssoufouHoto: AFP/I Sanogo

Magadan gari masu yawa ne suka shugabancin da’irar birnin Maradi ta Jamhuriyar Nijar dauko tun daga mulkin soja na rikon kwarya zuwa yanzu. Sai dai birnin da ke matsayin babbar cibiyar kasuwancin kasar ya tsinci kansa cikin wata matsala ta rashin iya jagoranci, lamarin da ya haddasa tsigewa da rushe majalisun koli na gudanar da mulkin jihar da da'irar birnin mai dadaden tarihi.

Wasu na danganta matsalar da rashin iya tafiyar da dukiyar jama'a, a yayin da wasu ke ta'allaka batun da dalilai na siyasa, daidai lokacin da wasu manazarta ke yi wa batun kallon cewa ka iya maida hannun agogo baya duba da yadda yanzu haka ake bin da'irar birnin bashi na kudade da suka kai sefa million dubu biyar. Alhaji Kabiru Sani Gonda manazarcin al’amuran yau da kullun ne a Maradi ya ce "Tsarin tsigewa ke daya amma dalilan da suka haddasa tsigewar sun banbanta. Ya zama wajebi a yanzu shugabannin siyasar da ake nadawa akan mukaman magadan gari musamman ma a Maradi su yi karatun tanatsu." 

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake tsige magadan gari ba a Jamhuriyar Nijar, galibi wadanda ake tsigewa ana zarginsu ne da aikata almundahana da dukiyar kasa, ko kuwa rashin iya jagoranci bayan gwamnati ta gudanar da bincike akan yadda suke tafiyar da aiki. A shekarar 2004 ce dai hukumomin kasar Nijar suka kaddamar tsarin bai wa yankuna da kananan hukumomi 'yancin tafiyar da mulkinsu, sai dai tun bayan kaddamar da tsarin an kama tarin shugabannin kananan hukumomi bisa zarginsu da aikata laifi, a yayin da a share daya masu adawa da tsarin ke zargin maye gurbinsu da 'yan jam'iyyar da ke mulki a wani mataki na share fagen manyan zabukan da ke tafe a kasar, a yayin da kungiyoyin farar hula ke matsa kaimi ga cewar ya zama tilas idan ana bukatar kaucewa matsalar a sake wani zaben kananan hukumomi domin ci gaba da kara wa wadanda ke aiki yanzu wa'adi wata dama ce ta keta haddin dimukuradiyya.