Nijar taƙaddama gabanin zaɓen ƙasar
January 29, 2016'Yan adawar sun ce dokokin tsarin mulki na ƙasar sun haramta wa sarakunan gargajiya shiga duk wani lamari na siyasa. To amma duk da hakan sarakunan na cikin harkokin siyasar ƙasar
Shigar sarakunan gargajiyar a cikin harkokin siyasa
Hon Abdoul Kadri Tidjani ke nan sakataren jam'iyyar MNSD NASARA mai adawa kuma kakakin ƙawancen jam'iyyun adawar ƙasar ke tabbatar da shigar da ƙarar majalisar sarakunan bisa zarginsu da taka rawa a cikin harkokin siyarsa domin goyon byan gwamnatin.
Kalamun na Tidjani Abdoul Kadri na zuwa ne 'yan kwanaki ƙalilan bayan aikewa da wata wasika da madugun 'yan adawar ya yi wa majalisar ta sarakunan gargajiya a tsakiyar wannan wata yana mai yi wa majalisar dama sarakuna da su guji yin shishigi ko nuna fifiko tsakanin wane da wane a fagen siyasa. Ganin irin rawa da ma matsayin da sarakunan suke da shi a bainar jama'a sai dai duk da hakan 'yan adawar sun ce sarakunan na ci gaba da aikata abin da 'yan adawar suka kira laifi ga dokokin tsarin mulki.
Shaidu na hanun sarakunan a cikin yaƙin neman zaɓe
'Yan adawar sun ce su ganau ne a kan wannan batu da gwamnati ke ɗauka a matsayin zargi,inda suka tabbatar cewar da anyi mahawara misali a jihar Maradi inda gwamna ya kira sarakunan gargajiya ya kuma umarcesu da su yi wa shugaban ƙasa mai ci yanzu, yaƙin neman zaɓe.Hon,Tidjani Abdoul kadri ya ce nan gaba idan har shari'a ta fara aikinta to duk wanni basaraken ko baruman da aka kama da aikata wannan laifin ya kuka da kansa.