SiyasaAfirka
Nijar za ta dauki dubban matasa aikin soja
November 30, 2020Talla
Ministan ya ce a karkashin wannan sabon yunkurin Nijar za ta kara yawan adadin sojojinta zuwa akalla dakaru 50,000 ko ma fiye da haka a cikin tsukin shekaru biyar.
A jawabin nasa na karshen mako, Issoufou Katambe ya ce a halin da ake ciki Nijar na da sojojin kasa guda 25,000 kuma bisa kiyasunsu kasar na bukatar dakarun soji 150,000 domin su samu damar yakar 'yan ta'adda yadda ya kamata.
Jamhuriyar Nijar dai na fuskantar kalubalen tsaro na mayakan tarzoma a yankin Diffa da ke makwabtaka da Najeriya, ga kuma rikicin da take yi da 'yan ta'adda da ke shigo mata ta kan iyakokinta da kasashen Mali da Burkina Faso.