Nijar: Babu jakkai a bisa kasuwani
September 24, 2019Talla
Daga daukar wannan doka a shekara ta 2016 zuwa yanzu kasuwancin jakkai a Nijar musamman a Maradi ya shiga cikin wani mawuyacin hali abin da ya jefa 'yan kasuwar jakkan da masu kiwon da sauran masu ci cikin harkar kasuwancin jakkan cikin matsaloli dabam-dabam. A bisa daukacin kasuwanin Maradi ba a samun jakkan kamar yadda aka saba gani a da, kana kuma farashinsu da a da ya tashi yanzu ya fadi saboda rishin ciniki.