1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Notre Dame: Duniya ta jajanta wa Faransa

Abdullahi Tanko Bala
April 16, 2019

Shugabannin kasashen duniya sun jajanta wa Faransa game da gobarar da ta kama a mujmi'ar Notre Dame mai matukar muhimmanci.

https://p.dw.com/p/3GtLL
Kathedrale Notre-Dame in Paris brennt
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Mattia

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta baiyana mujami'ar a matsayin wata alama ta al'adun Faransa da nahiyar Turai.

Shugaban Amirka Donald Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter yana cewa hotunan da aka gani da ke nuna yadda gobarar ta rika ci a cocin abin daga hankali ne kwarai.

Shi ma ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif ya baiyana jimami da aukuwar gobarar

Fadar vatican ta ce ta kadu matuka yadda gobarar ta yi ta'adi a mujami'ar da ke zama daya daga cikin wurare masu tarihi a duniya.

Shugaban majalisar gudanarwar Turai Donald Tusk yace tarayyar Turai na tare da Paris kan wannan iftila'i.

Shugaban majalisar dokokin tarayyar Turai Antonio Tajani ya yi bayani da cewa "Muna tare da Faransa da kuma Faransawa. Wannan abin da ya faru ba zai gushe cikin kankanin lokaci ba. Mun jaddada kudirin mu kuma mun yi maraba da shawarar yan majalisar dokoki na sanya wani asusu don tallafawa Faransa a kan wannan."

Shugaban faransa Emmanuel Macron ya sanar da kaddamar da gidauniya domin sake gina mujami'ar. Tuni ma wasu hamshakan attajiran Faransa su biyu suka yi alkawarin gudunmawa mai tsoka don sake gina mujami'ar.