090309 Obama Afghanistan
March 9, 2009Yanzu an samu canjin manufa a game da yaƙi a ƙasar Afganistan tsakanin yadda tsohuwar gwamanatin Amirka ƙarƙashin Jagorancin tsohon shugaba Bush da kuma sabuwar gwamnatin ƙarƙashin jagorancin sabon shugaba Barack Obama. Tsohon shugaba Bush dai yana ganin cewa, ya zama wajibi ga Amirka ta ci nasara a yaƙin da take yi a Afganistan, to amma tambayar da wani ɗan jarida da ke aiki da Jaridar New York Times yai wa Obama na cewa, shin shi ma Obaman yana ganin cewa ya zama wajibi sai an ci nasara ta hanyar yaƙi, ga dai Amsar da Obama ɗin ya bayar;
"A'a Sam-sam ba haka ba ne, amma na san cewa sojojinmu suna cikin hali na tsaka mai wuya, kuma suna fuskantar haɗarurruka a wannan yaƙi da suke yi."
Obama ya amsa tambayoyin manema labaran ne, yana mai amfani da wata na'urar zane-zane dake ofishinsa na shugabanaƙasa, inda ya zana musu taswirar yadda filin dagar da sojojin Amirka suke ya kasance, da yadda a kulli yaumin abubuwa sai ƙara taɓarɓarewa suke yi.
Obama ya ce, ''Yanayin yanzu ya zamanto mummuna, 'yan Taliban suna ƙara ƙarfi da yawa matuƙa gaya, kuma yanzu musamman ma a kudancin Afganistan sun canja salo na kai mana farmaki, ba kamar yadda muka sani a baya ba."
Tuni dai tattaunawa game da yarjejeniyar zaman lafiya tai nisa tsakanin sojojin Amirka da kuma 'yan gwagwarmayar Sunni, saboda 'yan sunnin sui aiki tare da sojojin Amirka, domin ai magani yadda ake samun ci gaba da tashe-tashen hankula daga ɓangaren dakarun Al-ƙa'ida a Iraƙi.
To sai dai halin da ake ciki a Iraƙi ya fi na Afganistan muni, yadda ake ganin cewa, daƙyar ne idan za a ga tasirin wannan tayin tattaunawar da Obama yai wa 'yan Taliban ɗin da ya kira masu sassaucin ra'ayi. Wanda inda ma ace a zamanin Bush ne, to an san cewa dama kwalliya ba za ta taɓa biyan kuɗin sabulu ba. Sheryl Gay Stolberg, wata 'yar Jarida ce dake aiki da Mujallar New York Times a Amirka.
"Ina ganin cewa wannan canji da Obama ya ɓullo da shi na tattaunawar sulhu da masu adawa da mu abu ne mai kyau, kamar yadda ya ƙuduri aniyar yi da ƙasar Iran da Afganistan, da kuma yadda ake tunanin yin irin wannan tattaunawa da ƙasar Siriya, dukkan waɗannan, matakai ne masu muhimmanci."
Kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar Amirka suka nunar, shi ma shugaban ƙasar Afganistan Hamid Karzai ya yi matuƙar maraba da wannan aniya ta Obama. Bayanai dai sun tabbatar da cewa, nan da watanni shida masu zuwa, za'a janye kimanin sojoji 12,000 daga Iraƙi, to amma a ɗaya hannun, Obama na shirin ƙara yawan sojoji a Afganistan.
Mawallafi: Klaus Kastan / Abba Bashir
Edita: Ahamad Tijani Lawal