1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta sha alwashin ganin bayan IS

Yusuf BalaDecember 7, 2015

Shugaba Obama ya bayyana cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an hana duk wanda aka haramtawa tafiye-tafiye mallakar makamai.

https://p.dw.com/p/1HINw
Frankreich Klimagipfel in Paris PK Obama
Shugaba Obama a lokacin da yake jawabiHoto: Reuters/K. Lamarque

A daren ranar Lahadi Shugaban Barack Obama na Amirka ya yi jawabi a ofishinsa wanda aka watsa kai tsaye inda ya dauki tsawon mintuna goma sha hudu yana jawabi ga 'yan kasar kan sabbin dabarun da Amirka za ta fitar na yaki da ta'addanci a duniya. Wannan na zuwa bayan harin da aka kai a California da ya yi sanadin rayukan mutane14.

Cikin jawaban da shugaban ya gabatar ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun bi 'yan ta'adda duk inda suke dan ganin bayansu. Ya ce za su yi aiki tare da sauran kasashen duniya da suka daura damara ta yaki da IS sai dai Amirka ba za ta sake sanya makudan kudadenta ba wajen jibge dakaru tsawon lokaci a yaki da 'yan ta'adda a kasashen Siriya da Iraki.

Har ila yau shugaba Obama ya bayyana cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an hana duk wanda aka haramta wa tafiye-tafiye ko wanda ake zargi ya mallaki bindiga.