1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama zai bayyana shirinsa kan mayakan IS

September 8, 2014

Ci gaban ayyukan masu tada kayar baya daga kungiyar masu jihadi ta IS ya sanya Amirka kara tsaurara matakai da za su kawo karshen kungiyar.

https://p.dw.com/p/1D8Xw
Obama gibt Statement zu Ferguson ab
Hoto: Reuters

Shugaban Amirka Barack Obama zai fara bayyana shirin sa na kawo karshen hare-haren kungiyar IS da ayyukansu ke kara tsamari a Iraki da kasar Syria.

Shugaban zai bayyana wadannan tsare-tsare na shi ne bayan ganawar sa da bangarori biyu na 'yan majalisa a fadar White House a ranar Talata, sannan ya gudanar da jawabi a ranar Laraba gabanin shirye-shirye na tunawa da ranar 11 ga watan Satimba da aka kai wa Amirkan harin ta'addanci a shekarar 2001.

Su dai mambobin majalisar na muradin ganin shugaba Obama ya zayyana irin ayyukan da ya ke son cimmawa kan mayakan na IS.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal