1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Biden zai bayyana tsarinsa na kiwon lafiya

November 10, 2020

Zababben Shugaban Amurka Joe Biden ya kuduri aniyar marawa tsarin kiwon lafiyar nan na Obamacare baya wanda Trump ya jingine.

https://p.dw.com/p/3l5La
USA Joe Biden mit Atemschutzmaske in Wilmington, Delaware
Hoto: Jonathan Ernst/REUTERS

Wannan na zuwa ne a yayinda ake sa ran kotun kolin kasar za ta saurari karar da aka shigar gabanta kan batun tsarin inshorar lafiya. A karkashin mulkin Shugaba Donald Trump dai tsarin Obamacare ya sha kashi, kuma an ta kai ruwa rana akai har ma daga karshe maganar ta je gaban kotu.

Kazalika nan gaba Mr. Biden zai yi jawabi kan batun kiwon lafiyar domin nuna muhimmancin da gwamnatinsa da yake shirin kafawa a watan Janairu za ta bai wa bangaren kiwon lafiya.

A jawabin da ya yi wa Amirkawa Joe Biden ya yi kira a gare su da kowa ya ajiye banbancin siyasa ya rinka sanya takunkumi domin a samu a yaki anobar coronavirus wace ta mamaye kasar.